Babban Limamin masallacin Jama’a na Usman Bn Affan dake Unguwar Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale,a jihar Kano Dr. Aliyu Muhammad Yunus, ya bukaci a gaggauta yanke hukunci mai tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a kashe-kashen da ake yi a ƙasar nan, yana mai cewa rashin hukunta masu laifi na ƙara ƙarfafa aikata ta’addanci.
Dr. Aliyu Yunus ya bayyana hakan ne yayin gabatar da hudubarsa ta ranar Jama’a 23 ga watan Janairu,2026 , inda ya nuna matuƙar alhini kan abin takaici da ya faru a unguwar Chiranchi, ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, inda wasu iyalan mutu daya gaba dayansu suka rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu wanda ya girgiza al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-allah-bai-halicci-duniya-domin-a-zauna-a-cikinta-ba-sheikh-daurawa/
A cewarsa, kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban nauyin da ke kan gwamnati, yana mai jaddada cewa duk wata gwamnati da ba ta iya cika wannan nauyi ba, to ta gaza a aikinta na shugabanci.
Ya bukaci hukumomin shari’a da su rika yin adalci cikin gaggawa, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a wannan mummunan lamari, da sauran makamantansa, ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada ba tare da wata tangarda ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-rashin-kamun-kai-daga-mata-a-wannan-zamanin-alama-ce-ta-tashin-kiyama-dr-aliyu-yunus/
Dr. Aliyu Yunus ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kamo masu laifi, yayin da ya bukaci al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Kano da ƙasa baki ɗaya.
Malamin ya kuma yi tsokaci kan ikirarin wasu gwamnonin Najeriya da a baya suka nemi Jama’a su Kare kansu matsayin gazawa karara kan sha’anin tsaro.

