Fitaccen malamin addinin Musulunci, a Najeriya Dr.Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ya yi karin haske kan girman hatsarin da ke tattare da aikata shirka ga Ubangiji, yana mai jaddada cewa babu wani abin da ya fi lalata imani da kyawawan ayyuka irin wannan zunubi.
Dr. Kabiru Gombe yayi wannan jawabi ne a yayin hudubar Juma’a da ya gabatar,a babban masallacin juma’a na Marigayi Sheik Abubakar Giro Argungun dake jihar Kebbi.
Dr. Gombe ya ce shirka ita ce babban abin da ke lalata imani gaba ɗaya, kuma tana gurgunta duk wani aiki na alheri da mutum ke yi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-masu-yada-jita-jita-na-daga-cikin-wadanda-suka-hana-najeriya-zama-lafiya-farfesa-rijiyar-lemo/
Ya ce saboda tsananin hatsarin ta ne malamai ke jan hankalin al’umma da su nesanta kawunansu daga duk wani aikin da zai kusantar da su ga wannan babban zunubi.
Ya yi nuni da cewa Musulmi ya kamata ya kasance cikin tsantseni, yana bincike da kula a cikin dukkan mu’amalolinsa don guje wa fadawa cikin shirkar da mutum kan aikata ba tare da sani ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubaan-koma-cin-mutuncin-addini-da-malamai-da-shugabanni-ta-hanyar-amfani-da-sabuwar-fasahar-ai-a-duniya-sheikh-sudais/
Dr. Gombe ya kuma yi gargadi ga al’umma su riƙa nazarin addininsu sosai, tare da neman karin ilimi a wuraren da suka dace, domin sanin halal da haram tare da fahimtar nauyin tauhidi a rayuwar Musulmi.
Ya ce, “Duk inda aka ga al’umma na fadawa cikin shirkar zamani, to ana iya hango raunana imaninsu da rikicewar dabi’u.”
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubaabinda-yafi-komai-dadi-a-aljanna-shine-ganin-allahmasu-ciyarwa-sune-a-gaba-dr-nasir/
Ya kammala da rokon Allah Ya tsare zukatan al’umma daga dukkan nau’ikan shirkar da al’adu ko jahilci ke haifarwa, yana mai kira ga mabiya addinin su dage wajen inganta tauhidi da tsarkake ibada ga Ubangiji Shi kaɗai.
TST Hausa ta rawaito cewa Dr. Gombe yaje Argungun ne domin daura Auren yayan Marigayi Shiek Abubakar Giro tare da aduar Allah ya gafarta masa

