Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tunatar da al’ummar Musulmi cewa Allah bai halicci duniya domin a mai da ita matsuguni na har abada ba, sai dai wurin jarrabawa da shiri zuwa rayuwar lahira.
Sheikh Daurawa ya bayyana hakan ne yayin hudubar da ya gabatar,a Masallacin juma’a na Jam’iar Skyline dake birnin Kano inda ya jaddada cewa rayuwar duniya mai wucewa ce, kuma dukkan abin da ke cikinta na gushewa ne, yayin da lahira ita ce madawwama.
A hudubar, malamin ya kawo misalai da dama kan yadda mutane ke ruduwa da son abin duniya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/buduba-cin-amana-da-yaudara-na-daga-cikin-abinda-zai-sa-allah-ya-zare-hannunsa-akan-mutum-ko-waye-farfesa-pantami/
Ya ce daga cikin alamun hakan akwai yadda wasu ke tara dukiya ta haram, suna cin amana ko zaluntar jama’a, amma idan aka tunatar da su mutuwa da lahira sai su ce “har yanzu lokaci yana nan”.
Yace wasu kuma na ruduwa da son abin hawa ko Mata da abinci ko abin sha da sauransu wanda yace a dalilin hakan ake kashe juna.
Sheikh Daurawa ya ce wasu kuma suna shagaltuwa da gina manyan gidaje da tara kadarori,wanda duka mutum a daki daya yake kwanciya.
Ya kara da cewa akwai mutanen da ke kashe makudan kudade wajen nuna jin dadi, da shagali da alfahari, amma su yi sakaci da taimakon marasa galihu,da marayu da mabukata.
Haka kuma, malamin ya ambaci misalin masu neman mukamai da iko, inda wasu ke yin karya, yaudara da haddasa fitina domin cimma burinsu, ba tare da la’akari da sakamakon hakan a lahira ba.
A cewarsa, wannan ma babbar alama ce ta ruduwa da son duniya fiye da yadda Allah Ya tanada.
Sheikh Daurawa ya kuma yi nuni da yadda wasu ke bata lokacinsu gaba daya a kafafen sada zumunta, suna neman yabo da daukaka daga mutane, amma su manta da neman yardar Allah.
Ya ce irin wannan hali na iya sa mutum ya manta da ibada da ayyukan alheri.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-rashin-kamun-kai-daga-mata-a-wannan-zamanin-alama-ce-ta-tashin-kiyama-dr-aliyu-yunus/
A karshe, malamin ya bukaci Musulmi da su dauki duniya a matsayin hanya, ba manufa ba; su yi aiki tukuru amma cikin halal, su rike amanar da Allah Ya ba su, tare da yawaita ayyukan alheri da za su amfane su bayan mutuwa.
Ya kuma nemi jama’a su rika maida hankali wajen gida rayuwar duniya data Lahira a lokaci guda

