Rahotanni na cewa akalla ma’aikatan gidan Talabijin na Kasa NTA a jihar Gombe guda shida ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata, sakamakon hatsarin mota da ya faru a Jihar Gombe.
Wadanda suka rasu sun hada da Manu Haruna Kwami, Manajan Gudanarwa da Zarah Umar, Manajar sashen Labarai; da Isa,wanda ya kasance Edita; da Musa Tabra, wanda ya kasance tsohon Manajan Labarai;da Aminu, shi kuma shine direba; da Adams, ma’aikacin Startimes.
Rahotanni sun bayyana cewa Emmanuel Akila (Manajan Labarai),da Jonathan Bara (Manajan Talla), da Steven Doddo (Babban Jami’in Talla) sun samu munanan raunuka kuma suna karbar kulawar likitoci a wani asibiti.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/matar-shugaban-kasa-ta-mikawa-gwamna-yusuf-tallafin-naira-miliyan-110-ga-iyalan-yan-wasan-kano-da-suka-mutu-a-hadarin-m
TST Hausa ta samu labarin cewa hatsarin ya faru ne yayin da Ma’ikatan ke komawa gida daga daurin auren wani ma’aikacin NTA Gombe akan hanyar Yola a jihar Adamawa.
Shugabanci da ma’aikatan NTA Gombe na cigaba da nuna alhini da jimami kan wannan mummunan lamari, inda suka roki Allah Ya bada hakurin rashin su.

