Gwamnatin jihar Lagos ta rufe babban masallacin Juma’a na al’ummar Hausawa da ke Agege a jihar Legas saboda rikicin shugabanci da Limanci.
Shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi shine ya bada umarnin rufe masallacin nan take bayan da aka yi artabu kan wanda zai rika jan Sallah.
Rikicin Limancin ya samo asali ne bayan rasuwar babban limamin masallacin Sheikh Sharif Habib Abdul-Majid, a ranar Larabar makon jiya.
A wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga yadda masallata da Limamin masallacin suka kaure da fada harda doke doke.
Akwai bangarori uku da ke da’awar neman shugabancin masallacin, da suka hada da iyalan marigayin da ya rasu da magoya bayansa sai bangaren Na’ibi wato Mataimakin liman da yayi ikirarin cewa shine zai gaji buzun liman
Sai Kuma na uku sarkin Hausawan Agege da yake ganin masallacin karkashin ikonsa yake ,kuma shine yake da hurumin nada liman.
Daya daga cikin jagororin addinin islama a Agege Sheikh Mahmud Shafi’i ya shaidawa Jaridar Daily Truth cewa rikicin ya haddasa hatta sallar Juma’a ta wannan makon ma ba’ayi ba.
Babban Sakataren majalisar sarkin Hausawan Agage Alhaji Abubakar Ali Na’ibi, yace sarkin Hausawan shine yake da IKon nada liman ko saukeshi.
Saidai shi kuma Mataimakin Liman malam Mustapha Imam Danlami, yace shine ya kamata ya gaji liman mai rasuwa.
Bugu da kari da aka tuntubi Shaikh Sharif Ismail Habib Abdul-Majid, dan marigayi babban limamin masallacin ya ki cewa komai, yana mai cewa har yanzu yana jimamin rasuwar mahaifinsa,amma sune ya kamata su rike masallacin.
Saidai karamar hukumar Agege tace ta rufe masallacin har sai abinda hali yayi dan gudun haifar da rikicin addini ,Inda Shugaban karamar hukumar Ganiyu Kola tace zasu gayyaci kowanne bangare domin zama dasu anan gaba.

