Gwamnatin jihar kano ta nemi shugaban ƙasa Bola Ahamad Tinubu da ya gaggauta bada umarnin dauke sarki Aminu Ado Bayero daga gidan Nasarawa a birnin Kano domin samun masalaha ga al’ummar jihar.
Gwamnatin ta ce a yanzu haka wasu na amfani da zaman Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Nasarawa domin cimma bukatun kansu musamman ma neman tayar da husuma a faɗin jihar.
Mataimakin gwamnan jihar kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan, a fadar gwamnatin Kano lokacin raba kayan tallafi da dan majalisar dokoki na Tarauni Hon Kabiru Dahiru Sule ya samar ,inda yace zaunar da sarkin kano na 15 a gidan sarkin na Nasarawa anyi shi ne da wata manufa domin hana gwamnatin kano ta zauna lafiya da kuma ƙin yiwa al’ummar jihar abin da ya dace.
Haka zalika kwamrat Aminu Abdussalam Gwarzo yace zanga-zanga da al’umma suka fito a wannan makon abu ne mai kyau tunda jama’a suna da hakkin fitowa domin nuna goyon bayan su kan abin da suke so, musamman nuna buƙatar a dauke sarkin kano Alhaji Aminu Bayero daga gidan Nasarawa amma aka turo jami’an tsaro suka hana su tare da kama wasu daga ciki.
Gwarzo ya kuma ce suna kira ga shugaban ƙasa da ya gaggauta ɗauke sarkin kano na sha biyar daga cikin jihar Kano domin barin al’umma su zauna lafiya.
Gidan Radio Freedom ya rawaito cewa gwamnatin kano ta ce yadda doka ce ta kawo tsohon sarkin haka kuma a yanzu doka ce ta kawo sabon sarkin dan haka abar doka tayi aikinta.

