Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da sabon Kwamiti na Musamman da zaiyi yaki da tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa matakan tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
An kafa kwamitin ne a ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, tare da haɗa wakilai daga hukumomin gwamnati,da ƙungiyoyin farar hula,da masana, da shugabannin al’umma.
A yayin kaddamar da kwamitin, Kwamishinan Yaɗa Labarai ya bayyana cewa tsattsauran ra’ayi na ci gaba da zama barazana ga tsaro da ci gaban Kano, lamarin da ya sa gwamnati ke ɗaukar matakan da suka haɗa da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-kano-ta-nemi-alumar-jihar-su-koma-ga-allah-domin-kubuta-daga-matsalolin-tsaro/
A yayin kaddamar da Kwmaatin Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya ce kwamitin zai yi aiki ne wajen tsara aiki na musamman da zai yi wa jihar jagoranci wajen magance Matsalolin tsaro ta hanyar haɗin kai, bincike, da fahimtar matsalolin da ke haifar da rikice-rikice daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Rubado.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/rashin-tsaro-gwamnonin-katsina-da-plateau-sun-rufe-makarantun-jihar-nan-take/
Kwamshinan Ibrahim Wayya yace irin wadannan masu tsaurin ra’ayin su ne ke shiga ayyukan ta’addanci a Najeriya ko ayyukan Daba
Ya kara da cewa a cikin watanni uku, kwamitin zai fitar da cikakken tsarin aiwatarwa wanda za a shigar da shi cikin Kwmaatin samar da zaman lafiya na Kano wanda ake sa ran kammalawa kuma kaddamarwa kafin tsakiyar 2026.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/yan-jarida-na-bada-gudun-mowa-kan-barazanar-tsaro-a-najeriya-inji-gwamnatin-tarayya/
Gwamnatin Kano ta nanata kudurinta na yin amfani da hanyoyi masu mutunta hakkin ɗan Adam, haɗin kan al’umma, da dabarun zamani wajen yakar tsattsauran ra’ayi da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Kwamared Wayya yace Kwamatin na yanzu ya hada da jami an tsaro da bangaren masarauta da kungiyoyin sa kai da sauransu.

