Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana ranar Juma’a 28 ga watan Nuwamba na shekarar 2025 matsayin ranar hutu ga ma’aikatan gwamnati, domin ba da damar gudanar da jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis.
A sanarwar da ta fito daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, gwamnati ta ce matakin na da nufin bai wa al’umma damar halartar addu’o’i da taron karrama marigayi malamin, wanda ya shafe shekaru yana wa’azi da yaɗa ilimin addini a fadin ƙasar nan.
Karin Labarai:https://tsthausa.com/5589-2/
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin jiha na tare da iyalan marigayin da dubban mabiyansa a wannan lokaci na jimami, tare da yi musu addu’ar Allah ya jikansa, ya gafarta masa, ya kuma bai wa iyalai hakuri da juriyar rashin.
Gwamnatin Bauchi ta kuma bukaci ma’aikata da al’umma su yi amfani da wannan rana wajen yin addu’a da tunawa da gudummawar da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayar wa addini da al’umma baki ɗaya.
A cewar sanarwar, za a yi jana’izar marigayin a Bauchi da misalin ƙarfe da za a sanar daga baya, inda ake sa ran dimbin mutane za su halarta.

