Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bukaci daukacin al’ummar jihar da su tashi da azumi gobe litinin da addu’a domin neman dawowar cikakken zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya ce ranar Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025, ita ce ya kamata duka al’ummar ta Borno su tashi da Azumi.
Zulum ya ce wannan mataki na da nufin neman tsarin Allah wajen kare al’umma daga masu tada fitina,da miyagun mutane, da dukkan makiyan zaman lafiya.
Karin labarai:https://tsthausa.com/gwamna-zulum-na-borno-ya-amince-a-sayar-da-man-fetur-naira-600-duk-lita-daya-a-jihar/
Ya bayyana cewa duk da cigaban da aka samu wajen tabbatar da tsaro a wasu yankuna, har yanzu ana fuskantar kalubale daga hare-haren Boko Haram da ISWAP, lamarin da ke bukatar hada karfi da addu’a da matakan tsaro.
Gwamnan ya kara jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro,da cibiyoyin tsaro na ƙananan hukumomi, da kungiyoyin fararen hula kamar CJTF, maharba da masu gadi domin inganta kariya a yankunan karkara.
Karin labarai:https://tsthausa.com/ramadangwamna-zulum-ya-dakatar-da-karbar-haraji-ga-yan-kasuwar-borno/
Zulum ya yaba wa mazauna jihar bisa jajircewar su da kuma yadda sukan goyi bayan irin wadannan bukatar al’umma na addu’a da azumi a baya. Ya ce hadin kan jama’a shi ne ginshikin samun ci gaba da wanzar da zaman lafiya a Borno.

