Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na jihar, Alhaji Ibrahim Namadi, kan rawar da ake zargin ya taka wajen bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Umarnin ya biyo bayan fushin jama’a da ya bulla bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa sunan kwamishinan ya fito a cikin wasu takardu na hukuma da suka shafi sakin wanda ake zargin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Don warware al’amarin, gwamnan ya kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike, ƙarƙashin jagorancin Barrista Aminu Hussain, mai ba shi shawara kan harkokin shari’a da dokokin kundin tsarin mulki.
An umurci kwamitin da ya gano hakikanin yadda al’amarin ya faru tare da bayar da shawarwari kan matakin da ya dace a ɗauka nan take.
Mambobin kwamitin sun haɗa da:
Barr. Aminu Hussain – Shugaba
Barr. Hamza Haladu – Memba
Barr. Hamza Nuhu Dantani – Memba
Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Memba
Manjo Janar Sani Muhammad mai ritaya – Memba
Comrade Kabiru Said Dakata – Memba
Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya
A yayin bayyana kwamitin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwa matuƙa kan zargin da aka yi, tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na yaki da shan miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u a cikin al’umma.

