Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci yaye matasa dubu biyu da dari biyu da sittin (2,260) da suka kammala koyon sana’o’i daban-daban a makarantun koyon sana’a ta jihar Kano.
TST Hausa ta rawaito cewa an baiwa matasan horo ne a cibiyoyin koyar sana’a da tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya samar guda 26.
Saidai a wajen taron gwamna Yusuf ya koka abisa yadda yace gwannatin da ta gabata ce ta rufe cibiyoyin ba tare da bude su ba, saida gwannatin sa tazo sannan suka dawo aiki.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-na-da-yancin-barin-nnpp-zuwa-apc-kamar-yadda-kwankwaso-ya-bar-pdp-zuwa-nnpp-shekarau/
A yayin taron yaye daliban Gwamna Yusuf ya rabawa kowannen matashi kayayyakin sana’a domin fara dogaro da kai.
An gudanar da bikin yaye daliban ne a budadden dakin taro na fadar gwannatin Kano inda gwamnan ga bayyana cewa shirin na daga cikin tsare-tsarensa na bunkasa kwarewar matasa, ds rage zaman kashe wando, da kuma habaka tattalin arzikin jihar.
Matasan sun samu horo a fannonin sana’o’i da dama, ciki har da kiwon Kifi da kiwon Kaji da harkokin fasaha da shuka tsirarai da kiwon dabbobi da sauransu.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf63-kana-mulkar-kanawa-akan-irin-akidar-malam-aminu-kano-cikin-tausayi-tinubu/
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa rabon kayayyakin sana’ar zai ba matasan damar fara sana’arsu kai tsaye, tare da samar da ayyukan yi ga kansu da ma sauran al’umma.
Ya kuma bukaci wadanda suka amfana da shirin da su yi amfani da damar da aka basu yadda ya dace, domin su zama abin koyi ga sauran matasa, tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar Kano gaba daya.

