Gwamnan Jihar Kano,Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ba mahaifin yaran da aka kashe da mahaifiyarsu a unguwar Chiranci Kwari kujerar aikin Hajji da Umara a matsayin tallafi da jaje bisa mummunan iftila’in da ya rutsa da iyalinsa ta hanyar kashe su.
Gwamnan Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yakai ziyarar ta’aziyya ga Mahaifin yaran guda shida wato Malam Haruna Bashir a kofar Nasarawa dake birnin Kano.
Gwamna Yusuf ya Kuma tabbatar da cewa za’a dauki matakin hukuncin Shari’a da ba a taba gani ba akan mutanan da aka kama da zarar an gurfanar da su.
Ya kuma godewa yan sanda da sauran hukumomin tsaro a Kano da suka bada gudun mawa waje kama matasan Uku.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da goyon bayan iyalan, tare da tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun zurfafa bincike domin gano tare da hukunta duk wadanda aka samu da hannu a kisan, kamar yadda doka ta tanada.
Yace Gwnanatin kano ta dauki nauyin baiwa mahaifin yaran ne zuwa aikin Hajji da Umara domin ya samu nutsuwa da kuma samun damar yi musu adua.
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya jikansu, Ya gafarta musu kurakuransu, Ya kuma ba iyalansu da al’ummar jihar Kano baki daya hakuri da zaman lafiya.

