Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin dakatar da rusau a garin Rimin Zakara dake karamar hukumar Ungogo a jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya bada umarnin ne a lokacin da yakai ziyara garin na Rimin Zakara.
Yace ya zama wajibi a dakatar da rusau din domin kare rayuwakan jama’a da dukiyoyinsu.
Yaci alwashin kawo karshen wannan turka turka da yace yasan ta dauki tsawon sama da shekara 30 ana fama da ita ,ta hanyar gayyatar kowanne bangare a zauna dasu.
Gwamna Yusuf ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
Bugu da kari gwamnan ya bada umarnin a gina sabon babban masallacin Juma’a a garin domin sadaukarwa ga wadanda suka mutu.
Sannan yace wadanda suka jikkata kuma, gwamnatin Kano zata cigaba da daukar nauyinsu har su warke.
Yace a yanzu haka an kafa kwamatin bincike akan wannan al’amari mara dadi.
Ya nemi al’ummar garin da su cigaba da baiwa gwamnati hadin kai domin samar da zaman lafiya.
Gwamnan yace a koda yaushe gwamnatinsa na kokari wajen kare rayuwakan jama’a da dukiyoyinsu.
Gwamna Yusuf ya kuma yi alkawarin samar da ayyukan raya kasa a garin na Rimin Zakara.

