Mummunar gobarar da ta tashi a kasuwar Singa da ke cikin birnin Kano, ta yi sanadiyar lalata dukiyoyi da kayayyaki da darajarsu ta kai sama da naira biliyan biyar (₦5bn), lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa cikin matsananciyar damuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta kama gine-ginen kasuwanci guda hudu masu dauke da shaguna da dama, inda wutar ta bazu cikin sauri sakamakon yawan kayayyakin da ke cikin shagunan.
Wasu gine-ginen sun kone kurmus, yayin da wasu suka samu mummunar barna.
Shugaban Kungiyat kasuwar, Junaid Zakari, ya bayyana cewa wannan gobara ta shafi rayuwar daruruwan mutane musamman wadanda kasuwanci shi ne kadai tushen samun kudinsu.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/babban-asibitin-rogo-ya-kama-da-wuta/
Ya yi kira ga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wa wadanda abin ya shafa domin su samu damar farfado da harkokinsu.
Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kano tare da sauran hukumomin tsaro sun shafe sa’o’i suna kokarin dakile yaduwar wutar kafin daga bisani a samu nasarar kashe ta gaba daya.
Sai dai a lokacin hada wannan rahoto, ana ci gaba da tantance girman barnar, tare da bincike kan musabbabin tashin gobarar.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru domin duba irin asarar da aka yi, tare da jajanta wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati za ta duba yiwuwar samar da tallafi domin rage radadin asarar da aka yi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/akwai-yiyuwar-man-fetur-yayi-karanci-a-yayinda-yau-1-ga-watan-marisdokar-hana-tankoki-masu-daukar-fetur-lita-60000-hawa-tituna-ta-fara-aiki/
Wasu rahotanni sun nuna cewa akwai mutanen da ake zargin sun bace a yayin gobarar, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike da kokarin tabbatar da tsaron yankin.
Gobarar ta haifar da cikas ga harkokin kasuwanci a yankin, yayin da ‘yan kasuwa ke kira da a dauki matakan kariya masu tsauri domin kauce wa maimaituwar irin wannan lamari a nan gaba.

