Tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirinsa na kafa sabuwar hukumar Hisbah mai zaman kanta domin bai wa jami’an Hisbah da aka sallama kusan 12,000 damar ci gaba da gudanar da ayyukan addini da kyautata tarbiyya a jihar.
Ganduje ya bayyana haka ne yayin karɓar kundin rahoton kwamitin da ya kafa domin tantance halin da jami’an da aka kora suka tsinci kansu.
Karin Labarai:https://tsthausa.com/6454-2/
Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da Hisbah masu kawar da badala da yan sa kai da masu bada shawarwari.
Kwamitin kafa sabuwar hukumar na karkashin jagorancin tsohon Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Dr. Harun Muhammad Ibn Sina,da tsohon Shugaban hukumar KAROT Hon. Baffa Babba Dan Agundi, da wasu manyan malamai.
Karin Labarai:https://tsthausa.com/6271-2/
TST Hausa ta rawaito cewa rahoton ya ƙunshi cikakkun bayanai da shawarwari kan hanyoyin farfado da ayyukan jami’an da aka kora, tare da tabbatar musu da makoma mai dorewa.

