Majalisar Matasan Arewa , tayi Allah wadarai tare da nuna rashin jin dadin ta akan matakin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya dauka na goyon bayan dokar Haraji ta 2024.
Matasan sunce Barau ya nuna karara ba cigaban yankin Arewa ne a gabansa ba .
A wata budaddiyar wasika ga Sanata Barau mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar tare da Sakatarensa, Dr. Mohammed Idris da Dr. Abdulhafiz Garba da sauran shugabannin kungiyar na a jihohi 19 sun ce Sanata Barau din baiyi la’akari da halin da Kano da sauran jihohin Arewa zasu fada ba idan har majalisar dattawa ta amince da dokar .
Matasan sun kuma ce, a matsayinmu na wakilan matasan Arewacin Najeriya, “mun yi imanin cewa kudurin dokar sake fasalin haraji, a halin yanzu, ba shakka zai yi illa ga tattalin arzikin kasa musamman Arewa .
Daga karshe Matasan Arewa sun shawarci Sanata Barau da ya canza tinani , kafin su hada dukkan al’ummar Arewa manya da matasa da yara da mata su dauki matakin da ya dace akansa da sauran masu goyon bayan dokar .
Sai dai Sanata Barau Jibrin ya mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi wa kudirin dokar harajin, inda ya musanta duk wani yunkurin yin zagon kasa ga Arewa .
A wani martani na sauti da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya yi karin haske cewa mutane ne basu fahimci dokar ba.

