Shugaban kungiyar matasan Famuyiwa da ke Jihar Ikko, Hon. Yahaya Gambo Ogan Boyen Gwarzo, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin matasan Arewa sun kai wani matsayi da za a rika gogayya da su ta fuskar tattalin arziki a fadin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da kungiyar ’yan jaridun Arewa a yankin Aja na Jihar Ikko.
Hon. Ogan Boyen Gwarzo ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da wasu matasan Arewa wajen aikata ayyukan da ba su dace ba, yana mai jaddada cewa yawancin fadace-fadace da ayyukan bata gari tsakanin matasa na da alaka da rashin ayyukan yi.
Ya ce wajibi ne ga masu hannu da shuni, ’yan kasuwa, da mahukunta su hada kai wajen samar da hanyoyin tallafa wa matasa, domin inganta rayuwarsu. Wannan ne kadai zai taimaka wajen rage ta’addanci da miyagun laifuka a kasa.
Ya kara da cewa, zuwa yanzu, ya samar wa dubban matasa ayyukan yi a sassa daban-daban na kasar nan, lamarin da ke sanya masa farin ciki da kwarin gwiwar ci gaba da wannan aiki na alheri.
Hon. Ogan Boyen Gwarzo ya bayyana cewa ya koya wannan dabi’ar taimakon matasa ne daga ogansa, Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano, Hon. Yusuf Umar Ogan Boye, wanda ya ce yana daga cikin matasan Arewa da ake alfahari da su.
Baya ga samar da ayyukan yi, Hon. Ogan Boyen Gwarzo ya ce yana mai da hankali kan bangarorin ilimi, lafiya da noma. Ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a raba littattafai sama da dubu uku tare da jakunkunan makaranta domin tallafa wa dalibai da inganta harkar koyarwa da koyo.
A nasa jawabin, Mai Unguwar Famuyiwa, Cif Abidadeen Kolapo, ya bayyana farin cikinsa kan gudummawar Hon. Ogan Boyen Gwarzo wajen ci gaban matasa da al’umma, ciki har da ayyukan addini da sauran shirye-shiryen raya yankin.
Ya yi kira ga sauran manyan masu hannu da shuni da ’yan kasuwa da su bi sahun Hon. Ogan Boyen Gwarzo wajen tallafa wa matasa da al’umma baki daya.

