Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta Jagorancin karrama Emeritus Farfesa J. Afolabi Falola, bisa gagarumar gudunmawa da ya bayar tsawon, sama da shekaru 40 a fannin ilimi,da bincike da horas da malamai, musamman rawar da ya taka wajen jagorantar malamai sama da goma da suka kai matsayin Farfesa a ƙarƙashin kulawarsa.
TEST Hausa ta rawaito cewa Emeritus Falola wanda ya fara aikin koyarwa a Jami’ar Bayaro a shakarar 1980 daga sashen nazarin Ilimin kasa wato Geography ya yaye dalibai 39 da suka kammala Karatun Digiri na uku (PhD).
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-kano-ta-nemi-tinubu-ya-gaggauta-bada-umarnin-dauke-sarkin-kano-na-15-aminu-ado-bayaro-daga-birnin-kano/
A yayin bikin karramawar,wanda tsaffin dalibansa suka shirya musaamman wadanda suka zama Farfesoshi da masu digiri na uku,jami’ar ta Bayaro ta bayyana cewa Emeritus Farfesa Falola ya taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙwarewar malamai, da inganta binciken kimiyya da kuma ɗaga martabar koyarwa a jami’ar, lamarin da ya taimaka wajen bunƙasa matsayin BUK a matakin ƙasa da na duniya.
Shugaban Jami’ar ta Bayaro Farfesa Haruna Musa ya ce Farfesa Falola ya shafe shekaru yana jagorantar bincike,da rubuce-rubucen kimiyya da kuma kula da ɗaliban digiri na biyu da na uku, inda da dama daga cikinsu suka zama manyan malamai, shugabanni da masana a jami’o’i daban-daban a Najeriya da wajen ƙasa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/dokar-harajidaliban-najeriya-zasu-iya-rasa-karatunsu-saboda-maganar-rushe-tetfund-a-cikin-dokar-haraji-inji-asuu/
Haka kuma, jami’ar ta jaddada cewa gudunmawar da Emeritus Farfesa Falola ya bayar ba ta tsaya ga koyarwa kawai ba, har da bayar da shawarwari kan tsara manhajojin karatu, kafa ƙungiyoyin bincike, da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i da cibiyoyin bincike.
Shugaban kwamatin shirya taron kuma daya daga cikin daliban Falola wato Farfesa Adamu Yusuf ya bayyana Emeritus Farfesa J. Afolabi Falola a matsayin abin koyi a ƙarni na yanzu musaamman ga matasa masu tasowa ya na mai cewa irin sadaukarwa,da gaskiya da jajircewa da ya nuna wajen gina ilimi da ɗan adam sun cancanci yabo da karramawa ta musamman.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/muna-gargadi-game-da-kokarin-siyasantar-da-ilimin-kasa-geography-a-najeriya-farfesa-badamasi/
Mahimman mutane daga sassa daban daban na Najeriya ne suka halarci taron karramawar ciki harda mai Martaba sarkin Nasarawa Alhaji Ibrahim Usman Jibril da wasu dalibansa daga Kasar Nijar.

