Tsohon ministan harkokin sadarwa da cigaban tattalin arziki na zamani,Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya jaddada cewa kyawawan dabi’u su ne tushen Addinin Musulunci, yana mai cewa babu cikakken imani face an haɗa ibada da kyakkyawar tarbiyya.
Farfesan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da hudubar Juma’a a Masallacin Indimi da ke birnin Abuja, inda ya bukaci Musulmi da su haɗa bautar Allah da nagartattun halaye kamar gaskiya,da rikon amana,da hakuri da adalci.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubasalon-sunan-gwamnatin-tinubu-na-muslim-muslim-bai-amfanar-da-musulmai-ba-sai-cutar-da-su-dr-aliyu-yunus/
Ya ce yawancin matsalolin da ake fuskanta a cikin al’umma na da alaƙa da sakaci wajen kyautata dabi’u,yana mai gargadin cewa Musulunci ya haramta munanan ɗabi’u irin su yaudara, da zalunci da cin amanar juna, komai girman matsayin mutum.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-babu-abin-da-ke-lalata-imani-kamar-shirkashi-ya-sa-hankalinmu-ke-tashi-kanta-dr-kabiru-gombe/
Pantami ya ƙara da cewa Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW), an aiko shi ne domin cika kyawawan dabi’u, yana mai kira ga iyaye,da malamai da shugabanni da su ba da muhimmanci wajen tarbiyyar al’umma, musamman matasa.
Hudubar ta samu karɓuwa daga masu ibada, kuma an wallafa cikakken bayaninta ta hanyar tashar Karatun Malaman Sunnah domin amfanin al’umma.

