An gano wani babban dalili da ya tilasta tsohon Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar,sauka daga mukaminsa.
Mai ba Shugaban Kasa shawara kan Bayani da Dabaru, Bayo Onanuga,shine ya sanar da cewa Badaru ya mika takardar ajiye aiki saboda “rashin lafiya.”
Sai dai binciken jaridar PUNCH ya nuna cewa Badaru ya sauka daga mukaminsa ne sakamakon rikici mai tsawo da yake faruwa tsakaninsa da karamin ministan tsaro Bello Matawalle, wanda aka boye wa jama’a na wasu watanni.
An nada Badaru a matsayin Ministan Tsaro ranar 21 ga Agusta, 2023, bayan kammala wa’adinsa na mulkin Jigawa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/rashin-tsaro-gwamnonin-katsina-da-plateau-sun-rufe-makarantun-jihar-nan-take/
An ce nadinsa ya dogara ne akan kwarewarsa a shugabanci da tasirin da yake da shi a yankin Arewa maso Yamma, musamman a lokacin da ake fama da karuwar ayyukan ‘yan bindiga da masu tada tarzoma.
Bayan nadinsa, Badaru ya mayar da hankali kan inganta kayan aikin soja, da gyaran sirri da ayyukan yaki da ta’addanci, yayin da Tinubu ya nada Matawalle domin ya tallafa masa wajen aiwatar da manufofin tsaro.
Sai dai a ‘yan kwanakin baya, rikicin tsakanin Badaru da Matawalle ya fito fili, musamman yayin da hare-haren ‘yan bindiga da ta’addanci suka karu, wanda ya tilasta Shugaba Tinubu sanar da sanya dokar ta baci a Najeriya.
Karuwar rashin tsaro ya kai ga sace dalibai da dama a jihohi da dama na Arewa, inda wasu masana ke kiran a sauke tsohon ministan saboda gazawarsa wajen jagorantar ma’aikatar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tura-ta-kai-bango-tsakanin-mu-da-yan-bindiga-da-ke-shigowa-kano-gwamna-yusuf/
Haka kuma, rikicin tsaron ya jawo hankalin duniya, musamman gwamnatin Trump wacce ta sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke takurawa Kiristoci da kashe shu a watan Oktoba.
Ana sa ran nan gaba za,a cigaba da fito da bayanai kan dalilan faruwar sabani tsakanin Badaru da Matawalle.

