Daga Muhammad Ali Yadakwari :
Kasa da wata daya bayan kaddamar da dawowar aikin matatar mai ta Fatakwal, yanzu rahotanni sun tabbtar dacewa matatar ta sake lalacewa ko ta tsaya cak bata aiki
Wani dan jarida, wanda ya ziyarci matatar a ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba, 2024, ya gano cewa bangaren dakon man fetur a matatar ya daina aiki komai ya tsaya cak.
A yayin da motocin dakon mai kusan 18 suka cika bakin titin da ke kan hanyar zuwa matatar an ga manyan motoci tara a cikin farfajiyar filin a ajiye, yayinda wajen daukar mai babu kowa.
Idan za’a iya tunawa anyi bikin kaddamar da matatar man ta Fatakwal ne wacce ke samar da ganga 60,000 a kowace rana ,a ranar 26 ga watan Nuwanba na shekarar 2024 wanda Shugaban kamfanin Mai na kasa NNPCL , Mele Kyari, ya jagoranta .
Hakan ya biyo bayan amincewa da kashe dala biliyan 1.5 a cikin watan Maris na shekarar 2021 domin farfado da matatar.
A yayin da ake sake bude matatar ta Fatakwal, an yi ta dakon man fetur zuwa cikin sassan kasar nan Inda yan Najeriya sukayi ta murna

