Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shaida hakan ne a wani taron liyafar cin abincin dare da gwamnatin Faransa ta shirya don karrama shi a fadar Palais des Elysée da ke birnin Paris a yammacin jiya Alhamis inda yace , babu gudu babu ja da baya a kan ingantaccen tsarin tattalin arziki da gwamnatinsa take amfani dashi a yanzu.
Tinubu ya nanatawa shugaban Faransa Emmanuel Macron cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara zai inganta tattalin arzikin Afrika, bama Najeriya ba.
Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga,shine ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar .
Wannan tsari na sauyin tattalin arziki a Najeriya munyi ne dan ceto dukan al’umar Nahiyar Afurika bama iya Najeriya kadai ba;inji Tinubu .
Tinubu ya kuma yaba wa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron kan sha’awar da yake da ita a nahiyar Afirka, wanda ya ce hakan zai kara karfafa alaka tsakanin kasashen biyu domin amfanar daukacin Nahiyar.
A jawabinsa, bayan kammala cin abincin daren ,Macron ya amince da shugabancin Najeriya a Afirka, tare da sanin rawar da take takawa a matsayin ‘babban yaya’ ga Nahiyar.

