Babban Kwamandan yan bijilanti na jihar Kano Alhaji Shehu Rabiu , ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su yi watsi da tsoron da suke yi wa ‘yan bata-gari, yana mai jaddada cewa tsoro ne ke bai wa masu aikata laifi damar ci gaba da addabar jama’a.
A wata ganawarsa da Rahma Radio ,Kano Shehu Rabiu yace sun dauki matakai kwarara akan tsare lafiyar Mutanan Kano da dukiyoyinsu dare da rana.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/matashin-da-ya-jagoranci-taaddancin-dorayi-shine-ake-zargi-da-kone-mata-biyu-a-tudun-yola-in-ji-yan-sanda/
Ya bayyana hakan ne bayan abinda ya faru a unguwar Chiranchi na kisan matar Aure da ya yanta shida.
Kwamandan ya ce ba za a taba cimma ingantaccen zaman lafiya ba matukar al’umma na jin tsoron fuskantar ‘yan daba da masu aikata laifuka.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/nawoj-a-kano-ta-yaba-wa-gwamna-yusuf-yan-sanda-kan-kama-wadanda-ake-zargi-a-mummunan-kisan-dorayi/
“Duk inda aka bar tsoro ya samu wajen zama a cikin jama’a to laifi zai yi karfi”In ji Shehu Rabiu.
“Dole ne mutanen Kano su yi jarumtaka, su daina kyale ‘yan bata-gari su rika tsoratar da su,” in ji Kwamanda Shehu.
Ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro, yana mai kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi cikin gaggawa, domin bai wa hukumomin tsaro damar daukar mataki cikin lokaci.
Kwamandan ya kuma tabbatar wa da al’ummar Kano cewa jami’an tsaro sun shirya tsaf domin dakile ayyukan bata-gari, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
A karshe, ya bukaci iyaye da shugabannin al’umma da su rika sa ido kan ‘ya’yansu, tare da taimakawa gwamnati da hukumomin tsaro wajen gina Kano mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

