Ana samun rahotanni cewa Babban Asibitin karamar hukumar Rogo, da ke jihar Kano, ya kama da wuta.
Shaidun gani da ido sun shaidawa TST Hausa cewa gobarar ta tashi ne a ɗaya daga cikin sassan asibitin, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin marasa lafiya da ma’aikata.
Wani maikataci a Asibitin Nasiru Adamu, ya shaida cewa babu wani maikataci ko mai jinya da marasa lafiya da suka rasu ko jikkata.
Yace gobarar ta fara ne daga dakin Ajiye mata marasa lafiya da bangaren Toyota.
Jami’an kashe gobara sun isa wurin da gaggawa domin bada taimako, inda ake ci gaba da kokarin takaita yaduwar wutar.
Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, kuma hukumomi ba.

