Rahotanni daga Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH),ya nuna cewa an samu billar cutar zazzabin lassa abinda ya haifar razani tsakanin jama’a.
Saidai tuni jami’an lafiya suka dukufa cikin gaggawa, domin dakile yaduwar cutar ciki har da gano mutanan da sukayi mu’amula da mutanan da suka kamu da cutar ta lassa.
Mai magana da yawun sashin kula da rigakafin kamuwa da cututtuka na asibitin AKTH Salisu Inuwa ya tabbatar da billar cutar ta Lassa kuma tuni aka killace mara lafiyan.
Inuwa yace a makon da ya gabata ne aka samu rahoton cewa an kai wasu mutane biyu da ake zargin suna dauke da cutar Lassa.
Yace mutum na farko ya rasu kafin a dauki jininsa a gwada a dakin gwaje gwaje na Asibitin.
TST Hausa ta rawaito cewa mutum na biyu wanda ya kai kansa Asibitin na AKTH da kafarsa an dauki jininsa kuma an gwada an gano yana dauke da cutar ta Lassa.
Mutumin wanda aka boye sunansa ya fito ne daga karamar hukumar Garun Malam.
Bayan tabbatar da billar cutar ta lassa Asibitin na AKTH ya fitar da tsare tsare na gaggawa domin kare kai ciki harda fara tantance mutane domin riga kafi.
Rahotanni nacewa an sanya ido akan wasu ma’aikata da sukayi mu’amula da marasa lafiyan wadanda a yanzu suke dauke da alamar zazzabi.
A shekarar 2024 an samu mutane 1,005 da suka kamu da cutar Lassa a jihohin 28 daga cikin 36

