Jami’an tsaro a Masallacin Harami sun cafke wani mai ibada bayan an hango shi yana yin sallah a saman wani shinge (railing) a cikin harabar masallacin.
Lamarin, wanda ya faru a daren 27 ga watan Ramadan saboda cikowar jama’a ya janyo hankalin jami’an tsaro, inda suka gaggauta daukar mataki domin kauce wa duk wani hatsari.
Rahonni nacewa an yi cikar kwari a ciki da wajen Masallacin na Harami saboda neman dacewa da daren lailatul Qadari.
KARIN LABARAI:Har Yanzu Akwai Dama Ta Neman Daren Lailatul Qadr — Limamin Harami A Makkah Ya Ja Hankalin Musulmi A Juma’ar Karshe Ta Ramadan
Rahotanni sun bayyana cewa tsayuwa a irin wannan wuri mai tsawo na iya jefa mutum cikin haɗarin fadowa, tare da yiwuwar haddasa firgici ko rudani a cikin taron jama’a.
TST Hausa ta rawaito cewa Mahukunta sun sake jaddada cewa, duk da girman darajar ibada a wannan wuri mai tsarki, wajibi ne a bi ƙa’idojin tsaro da aka shimfiɗa domin kare rayuka da tabbatar da tsari mai kyau.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/an-gudanar-da-sallar-rokon-ruwa-a-saudiyya/
Ba wai an hana shi ibada ba ne, sai dai an dauki mataki ne saboda wurin da ya zaba yana da haɗari ga shi da sauran jama’a.
Tuni Mahukuntan Saudiya suka saki Mutumin bayan tsare shi na dan wani lokaci tare da jan kunnensa.

