An kaddamar da takardar fara daukar dakarun hukumar Hisbah Gandujiyya mai zaman kanta a Kano.
Anyi bikin fara raba takardar ne ƙarƙashin jagorancin jigon jam’iyyar APC a jihar, Baffa Babba Dan Agundi, tare da tsohon kwamandan Hisbah na jihar, Sheikh Harun Ibn Sina.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kalaman-ganduje-na-kafa-hisba-da-na-barau-akan-cigaban-kano-su-ne-suka-janyo-rashin-tsaro-a-jihar-gwamnatin-kano/
Bikin kaddamarwar ya samu halartar dimbin matasa masu sha’awar shiga rundunar, inda aka yi bayanai kan ka’idoji,da sharudda da kuma aikace-aikacen da ake buƙata daga masu nema.
A cewar Dan Agundi, shirin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙara inganta tsaro da kula da ɗabi’un al’umma a jihar.
Shi ma a nasa jawabin, Sheikh Harun Ibn Sina ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa rundunar Hisbah na taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da natsuwa, gudanar da sulhu, da kuma wayar da kai game da kyawawan ɗabi’u a tsakanin al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ganduje-zai-kafa-sabuwar-hukumar-hisba-mai-zaman-kanta-a-kano/
A cewar masu shirya taron, ana sa ran fara tantance masu nema da karɓar waɗanda suka cika ƙa’idoji nan bada jimawa ba.
TST Hausa ta rawaito cewa tun a makonnnin da suka gabata ne gwamnatin Kano tayi Allah wadarai da ikirarin samar da Hisbar mai zaman kanta inda gwamnatin tace hakan ya Saba doka.

