An kaddamar da Mata Media,wata kafar yada labarai ta mata Zalla wacce ke aiki cikin harshen Hausa kuma irinta ta farko a Najeriya domin ba da labarai da tattaunawa kan al’amuran da suka shafi mata, da aka samar saboda mata da kuma domin mata.
An kafa kafar yada labarai ta Mata Media ne daga ƙwararrun mata ‘yan jarida masu gogewa, domin inganta rawar mata a fagen jarida, da ƙarfafa muradunsu, da kuma ƙalubalantar ra’ayoyin da ke tauye ci gaban mata ta hanyar samar da ingantattun rahotanni.
“Kaddamar da Mata Media babban mataki ne wajen cike gibin da ke fagen jarida a Najeriya, musamman wajen ba mata dandalin da muryoyinsu za su ƙara ƙarfi,” in ji Fauziyya Kabir Tukur, Manaja Darakta kuma daya daga cikin masu kafa jaridar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/na-yafewa-maryam-sanda-kuma-na-goyi-bayan-afuwar-da-tinubu-ya-yi-mata-in-ji-mahaifin-mijinta/
Tace “Burimu shi ne samar da tsari mai aminci da natsuwa, inda mata za su iya bayyana labarunsu, ra’ayoyinsu da hangen nesansu cikin ‘yanci.”
Kafar jaridar ƙarƙashin jagorancin Fauziyya Kabir Tukur tare da Hafsat Bahara a matsayin Edita, za ta rika wallafa labarai,da nazari, rahotanni na musamman da bayanai kan wasan da mata ke takawa a al’umma, da ƙalubalen da suke fuskanta.
Mata Media ta kuma zayyana shirin haɓaka ƙarni na gaba na mata ‘yan jarida ta hanyar bai wa matasa da masu sha’awar aikin jarida damar koyon aiki da tarbiyya a fannin.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/an-sace-amarya-da-kawayenta-14-a-sokoto-a-yayin-biki-yau-lahadi/
A mataki na farko, cibiyar za ta kasance kafar a dandalin yanar gizo kaɗai, tare da kasancewa a Facebook, da Instagram, da TikTok,da YouTube, da kuma shafin yanar gizo.
Sanarwar ta ce Jama’a na da damar bin shafukan domin samun sabbin labarai da kayatattun shirye-shirye da suka shafi mata.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/inaji-kamar-na-fashe-da-kuka-idan-naga-ana-cin-zarafin-yaya-mata-a-najeriya-huriyya-dauda-lawan-dare/
Sanarwar tace “Muna gayyatar abokan hulɗa, hukumomi da sauran kafafen jarida da su yi aiki tare da mu domin ƙara ɗaukaka muryar mata a Najeriya,” in ji Manaja Daraktan.

