Majalisar koli kan harkokin addinin Musulunci a Najeriya ta sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2026 a wasu sassan Najeriya.
A wata sanarwa da Sakataren kwamatin gani Farfesa Sambo Wali Junaid ya fitar yace mai martaba Sarkin Borno Alhaji (Dr.) Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi shine ya sanar da ganin watan a madadin sarkin Musulmi wanda yake balaguro zuwa kasashen waje.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/an-ga-watan-azumin-ramadana-a-saudiyya/
A jawabin da ya yi na sanarwar wanda aka sanya a shafin Tuwita na kwamitin ganin watan, Sarkin na Borno ya ce an ga watan ne bayan samun rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci da ke wasu jihohin ƙasar.
Hakan na nufin gobe Laraba 18 ga watan Fabareru na shekarar 2026 za ta kasance daya ga watan Ramadan.
Allah ya karbi Ibadunmu.. .

