Daraktan shirya wasan kwaikwayo,Prince Daniel Aboki, ya sanar da cewa an kammala dukkanin bin ka’idoji da sahalewar doka da suka wajaba, domin fara aikin shirya fim ɗin “Maitatsine” a hukumance.
KARIN LABARA:https://tsthausa.com/matar-shugaban-kasa-ta-mikawa-gwamna-yusuf-tallafin-naira-miliyan-110-ga-iyalan-yan-wasan-kano-da-suka-mutu-a-hadarin-m
A cewarsa, an samu cikakkiyar amincewa daga hukumomin da abin ya shafa, domin haka babu wani shinge da zai hana fara ɗaukar fim ɗin yanzu.
Fim ɗin zai waiwayi rayuwar Muhammadu Marwa, wanda aka fi sani da Maitatsine, da kuma tasirin kungiyarsa ta ’Yan Tatsine wadda ta haddasa rikice-rikice a wasu sassan Arewacin Najeriya a shekarun 1980.
Daraktan ya bayyana cewa fim ɗin na daga cikin manyan ayyukan shirya fina-finai a kasar nan , inda ake sa ran zai haɗa dubban ‘yan wasa da ma’aikata, domin a fayyace abubuwan da suka faru cikin tsari na tarihi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-ya-amince-da-nadin-sani-musa-danja-a-matsayin-mai-bashi-shawara-kan-matasa-da-wasanni/
Ya kuma jaddada cewa hoton da ya karade kafafen sada zumunta game da fim ɗin, na’urar fasahar kere-kere ce ta (AI), kuma ba hoton tallan fim ɗin na asali ba ne.
TST Hausa ta rawaito cewa masu shirya fim ɗin na fatan aikin zai taimaka wajen ilmantar da al’umma da kuma zurfafa fahimta kan wannan muhimmin babi na tarihin Najeriya, tare da jawo hankali kan illolin tsattsauran ra’ayi da tashin hankali.

