Marigayin Alhaji Bature Abdulaziz ya kasance fitaccen bawan Allah, mai kyakkyawar mu’amala da jama’a, wanda ya bayar da gudunmawa mai yawa a rayuwarsa, musamman a fannonin da suka shafi al’umma da ci gaban jama’a.
Wannan rasuwa ta jefa iyalai, abokai da al’umma cikin jimami da alhini.
Ana sa ran za a sanar da lokaci da wurin sallar jana’iza, da kuma makwancin marigayin, da zarar an kammala tanadi.
KARIN LABARAI: https://tsthausa.com/tinubu-da-gwamnonin-arewa-sun-bada-hutu-a-najeriya-saboda-rasuwar-buhari/
Muna roƙon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma ba iyalansa, ‘yan uwa da masoya haƙuri da juriyar wannan babban rashi.

