Tsohon dan majalisar Dattawa na Kogi ta yamma Sanata Dino Melaye ya yi martani kan gurfanar da tsohon Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), a gaban kotu bisa zargin handame kudade da halasta kudin haram.
Melaye, a shafinsa na sada zumunta ya wallaca ceqa shari’ar da ake yi wa Malami ta tunatar da shi irin kalubalen shari’o’in da ya fuskanta a lokacin da Malami ke rike da mukamin Ministan Shari’a, inda ya ce a wancan lokaci an sha gurfanar da shi kan tuhume-tuhumen da ya bayyana a matsayin na siyasa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/babu-wanda-ya-kama-ni-ni-na-kai-kaina-efcc-inji-tsohon-jamiin-nnpc/
Duk da haka, Dino Melaye ya ce yana yi wa Malami fatan alheri, yana mai cewa rayuwa tana da juyayi, kuma kowa na iya fuskantar irin wannan hali a wani lokaci na daban.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar Talata ne Hukumar EFCC ta gurfanar da Abubakar Malami tare da ɗansa,Abdulaziz Abubakar Malami, da Matarsa da wani mutum, a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, kan tuhume-tuhume guda 16 da suka shafi handame kudade da mallakar dukiyoyi ta haramtacciyar hanya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/bamu-taba-yin-katsalandan-a-aikin-hukumar-yaki-da-cin-hanci-ta-kano-ba-gwamna-yusuf/
Wadanda ake tuhuma sun musanta laifukan, yayin da kotu ta aike da su gidan gyaran hali na Kuje, tare da dage sauraron buƙatar beli zuwa ranar 2 ga Janairu, 2026.
Dino Malaye yace Malami lokacin yana ministan Shariah ya taka rawa wajen kuntata masa, amma sai gashi yau Reshe ya juye da mujiya

