Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta gudanar da wani zama na musamman da ya kunshi yin Wa’azi ga wasu ’yan siyasa da suka shahara wajen magana a kafafen yaɗa labarai, waɗanda aka fi sani da Sojojin Baka, domin faɗakar da su kan illar cin mutuncin juna a shafukan sada zumunta.
Zaman sulhu da faɗakarwar ya zo ne bayan gano yadda wasu daga cikin ’yan siyasar ke jifan junansu da munanan kalamai waɗanda ba su dace ba, sakamakon saɓanin siyasa da ke tsakaninsu. Ana ganin irin waɗannan kalamai na taɓa mutuncin juna, da kimar iyaye, da martabar Jihar Kano, har ma da ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci zaman da aka gudanar a ofishin hukumar da ke Kano, a ranar Alhamis.
Manyan ’yan siyasa da dama ne suka halarci zaman, ciki har da Alhaji Nagoda, Ali Gyara Hausawa, Gamboliya Ja’en, da kuma wakilin Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, tare da sauran ɓangarorin siyasar.
Saidai TST Hausa ta rawaito cewa ba’a ga fuskar A’in Jafaru daga bangaren kwankwasiyya ba.
A yayin zaman, Sheikh Abbas Abubakar Daneji ya bayyana cewa an gayyaci ’yan siyasar ne domin faɗakar da su kan illar amfani da munanan kalamai a tsakaninsu, tare da sulhunta su da samar da mafita mai ɗorewa.
Shi ma Kwamishina na Biyu a Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya ce hukumar ta shirya zaman ne domin nemo mafita kan rikicin da ke tsakanin ɓangarorin ’yan siyasar, musamman dangane da munanan kalaman da suke yi wa junansu.
A nasu jawaban, Alhaji Nagoda da Ibrahim Soja Kantin Kwari sun bayyana cewa daga wannan lokaci ba za a sake samun su suna cin mutuncin wani a harkokin siyasa ba.
Haka kuma, Ali Gyara Hausawa da Gamboliya Ja’en, waɗanda suka shafe kusan shekaru uku ba tare da magana da juna ba sakamakon saɓanin siyasa, sun samu damar sulhu a yayin zaman, inda suka yafe wa junansu.
An gudanar da zaman ne a gaban wakilin Daraktan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS reshen Jihar Kano, da wakilin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, da wasu daga cikin shugabannin hukumar gudanarwa ta Hukumar Shari’a, da Kwamishina na Ɗaya a hukumar, da daraktoci, da kuma ɗimbin ’yan siyasa, musamman waɗanda suka fi fuskantar saɓani da juna sakamakon munanan kalamai a kafafen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta.

