Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, wanda aka fi sani da Majiɗaɗin Kiru, ya bayyana yadda gwamnatinsu ta mayar da dubban ƙwararrun malamai zuwa makarantun gwamnati domin magance ƙarancin malamai da ake fuskanta, duk da ƙalubalen ƙarancin kuɗaɗen da gwamnati ke samu.
Majiɗaɗin Kiru ya bayyana cewa sun mayar da malamai sama da 5,900 waɗanda aka tura aiki zuwa azuzuwa, yayin da aka kuma dawo da malamai sama da 6,900 waɗanda gwamnati ke biyan albashinsu amma suke koyarwa a makarantu masu zaman kansu.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da ɗaya daga cikin kafafen yaɗa labarai na zamani.
Tsohon kwamishinan ya ce an ɗauki matakan ne domin magance ƙarancin malamai a makarantun gwamnati, a lokacin da gwamnatin jihar ke fuskantar matsalolin kuɗi da suka hana ta ɗaukar sabbin ma’aikata yadda ya kamata.
A cewarsa, wani bincike da Ma’aikatar Ilimi ta gudanar ya gano cewa wasu makarantun gwamnati suna da malami guda ɗaya kacal, wanda shi ne shugaban makarantar, duk da cewa akwai ɗalibai da dama da suke buƙatar koyarwa.
Ya ce: “A ƙaramar hukumata ta Kiru kaɗai, akwai makarantu sama da 57 zuwa 59 waɗanda shugaban makaranta ne kawai yake koyar da dukkan ɗaliban makarantar.”
Majiɗaɗin Kiru ya bayyana cewa daga bisani ma’aikatar ta haɗa kai da sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomi da daraktocin shiyya domin gano hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar.
Ya ce binciken ya gano ƙwararrun malamai masu takardar shaidar koyarwa ta NCE da kuma waɗanda suka kammala digiri a fannin ilimi, waɗanda aka tura aiki a ofisoshin gudanarwa, ƙananan hukumomi da wasu hukumomin gwamnati maimakon su kasance a azuzuwa.
A cewarsa, ma’aikatar ta dawo da waɗannan malamai tare da mayar da su azuzuwan koyarwa, baya ga malaman da gwamnati ke biyansu albashi waɗanda aka tura zuwa makarantu masu zaman kansu.
Ya jaddada cewa wannan mataki ya taimaka wajen ƙarfafa harkokin ilimin gwamnati, tare da nuna muhimmancin inganta yadda ake amfani da ma’aikatan da ake da su, musamman a lokacin da ake fuskantar matsalolin ɗaukar sabbin malamai.
Tsohon kwamishinan ya ƙara da cewa ba za a iya auna tasirin gyare-gyaren da ake yi a harkar ilimi nan take ba, domin inganta koyarwa da koyo yana buƙatar ci gaba da zuba jari da kuma ba da lokaci.
ANNOBAR CUTAR COVID-19 DA CI GABAN MAKARANTU
Da yake waiwayen lokacin da ya riƙe muƙamin kwamishinan Ilimi, Majiɗaɗin Kiru ya ce gwamnatinsu ta ƙaddamar da sabbin shirye-shiryen inganta ilimi, ta kafa sabbin makarantu, ta gyara waɗanda ake da su, sannan ta shirya horaswa ga malamai.
Ya bayyana cewa yawan al’ummar Jihar Kano na ƙara matsin lamba ga gine-gine da sauran kayayyakin more rayuwa na makarantu, inda ya ce a lokacin jihar tana da sama da makarantun firamare 8,000 da kuma kusan makarantun sakandare 1,548.
Ya ce gwamnati ta kuma ɗauki matakan tabbatar da ci gaba da karatu a lokacin annobar COVID-19, ta hanyar amfani da shirye-shiryen talabijin da rediyo domin isar da darussa ga ɗalibai, bayan da aka samu tsaiko a tsarin karatun da ake yi a azuzuwa.
Sauran matakan da ya ce an ɗauka sun haɗa da samar da kayan koyarwa, ɗaukar ƙwararrun waɗanda suka kammala karatu, ƙarin girma ga malamai da kuma tabbatar da biyan albashinsu a kan lokaci.
Sai dai ya bayyana ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da suka addabi ɓangaren ilimi a lokacin da yake kwamishina.
Majiɗaɗin Kiru ya ce ƙarancin kuɗaɗen da ake warewa gwamnati a wancan lokaci ya rage mata damar ɗaukar sabbin ma’aikata, bayan biyan albashi da sauran muhimman buƙatun gwamnati.
Ya bayyana cewa matsin tattalin arziƙin ne ya sa suka zaɓi wasu hanyoyin magance ƙarancin malamai, maimakon dogaro kawai da ɗaukar sabbin ma’aikata.
Tsohon kwamishinan ya kuma amince da ƙoƙarin gwamnatin yanzu na ɗaukar sabbin malamai, yana mai cewa wannan mataki ya ƙara yawan ma’aikatan da ake da su a makarantun gwamnati.
Ya danganta ƙarin ɗaukar malamai da aka samu da ingantuwar kuɗaɗen shigar gwamnati, tare da bayyana kyakkyawan fata kan makomar ilimi a Jihar Kano.
MAYAR DA ABBА KABIR YUSUF APC CI GABA CE MAI KYAU.
Da yake tsokaci kan siyasar Jihar Kano, Majiɗaɗin Kiru ya bayyana komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC a matsayin ci gaba mai kyau, yana mai cewa hakan na nufin ci gaba da tasirin siyasar jam’iyyar a jihar.
Ya ce yana cikin APC tun lokacin da aka kafa jam’iyyar a shekarar 2014, bayan haɗewar wasu jam’iyyun siyasa da suka haɗa da ACN,da CPC da ANPP.
A cewarsa, APC ce ta riƙe mulkin Jihar Kano har zuwa shekarar 2023, lokacin da ta sha kaye a zaɓen gwamna a hannun jam’iyyar NNPP.
Ya bayyana cewa komawar gwamnan APC ta ƙara wa jam’iyyar ƙarfi tare da samar da damar haɗin gwiwar siyasa tsakanin mambobinta.
Da aka tambaye shi kan korafe-korafen wasu tsofaffin mambobin APC na cewa ana nuna musu wariya bayan komawar gwamnan jam’iyyar, tsohon kwamishinan ya ce shi da mutanensa ba a ware su daga harkokin jam’iyyar ba.
Ya yi nuni da matsayin mataimakin gwamnan jihar na yanzu, wanda ya bayyana a matsayin ɗan ƙungiyar siyasarsu, yana mai cewa sun taɓa yin aiki tare a matsayin kwamishinoni a gwamnatin jihar.
Majiɗaɗin Kiru ya kuma ambaci naɗa wasu masu ba da shawara daga cikin mambobin APC, yana mai cewa irin waɗannan naɗe-naɗe na nuna cewa ana ba wa waɗanda suka ci gaba da kasancewa a jam’iyyar damar shiga harkokin mulki.
Ya ƙara da cewa an kafa kwamitoci a matakin ƙananan hukumomi domin bai wa ’yan siyasar da suka taɓa riƙe muƙaman gwamnati damar shiga harkokin jam’iyyar.
A cewarsa, tsofaffi da kuma waɗanda ke kan muƙaman shugabannin ƙananan hukumomi, ’yan majalisar jiha da ta tarayya, kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, sakatarorin zartarwa, manajojin gudanarwa da daraktoci-janar na daga cikin waɗanda za su iya shiga kwamitocin.
Ya ce waɗannan tsare-tsare sun samar da dama ga gogaggun ’yan siyasa su bayar da gudummawa wajen yanke shawara da kuma bunƙasa al’umma.
Tsohon kwamishinan ya amince cewa rashin jituwa da korafe-korafe ba za su rasa faruwa a siyasa ba, musamman idan wasu mutane suka ji cewa ba a cika musu burinsu ba.
Sai dai ya jaddada cewa ya kamata a duba ko mambobin jam’iyya suna da wakilci a tsarin yanke shawara wajen tantance ko ana ba su damar shiga harkokin jam’iyyar.
Ya ce: “Babu wani mutum da zai iya gamsar da kowa sai Allah. Amma muna ƙoƙarin yin adalci gwargwadon ƙarfinmu.”
DALILIN DA YA SA NA SHIGA SIYASA
Da yake bayyana dalilin da ya sa ya shiga siyasa bayan ya yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnati, Majiɗaɗin Kiru ya ce shiga siyasa na samar da babbar dama ta bayar da gudummawa ga ayyukan gwamnati da ci gaban al’umma.
Ya bayyana ra’ayinsa cewa ya kamata masu ilimi da gogewa su shiga siyasa, maimakon su tsaya a gefe suna sukar manufofin gwamnati da yadda jami’an gwamnati ke gudanar da ayyukansu.
A cewarsa, mutanen da suka fahimci yadda hukumomin gwamnati ke aiki za su iya bayar da gudummawa mai amfani wajen tafiyar da mulki ta hanyar ba da shawarwari, karɓar nauyin gudanar da ayyuka da kuma taimakawa wajen tsara manufofin gwamnati.
Ya ce gogewar da ya samu a aikin gwamnati ta ƙara masa sha’awar yi wa al’umma hidima, musamman ta fuskar samar da ayyukan yi ga matasa.
Majiɗaɗin Kiru ya ƙara da cewa damar taimaka wa jama’a a lokacin da yake aikin gwamnati ta sa ya yi tunanin irin gudummawar da zai iya bayarwa idan ya samu muƙamin siyasa ta hanyar zaɓe ko naɗi.
Ya kuma bayyana cewa riƙe muƙamin siyasa na iya samar da damar jawo ayyukan ci gaba zuwa ga al’ummar mutum da kuma yankin da ya fito.
Tsohon kwamishinan ya tsaya takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a zaɓen shekarar 2023, amma bai yi nasara ba.
A halin yanzu, yana riƙe da muƙamin Daraktan Horaswa da Shirye-shirye a Cibiyar Ci Gaban Jam’iyyar APC, wato Progressive Institute (TPI), inda ya ce yana ci gaba da shiga harkokin siyasa da ayyukan jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

