Wata kotu a jihar Bauchi ta yanke wa wasu mutane takwas hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari kowannensu, bayan samunsu da laifin daba da kuma tayar da hankulan jama’a a unguwar Dim da ke cikin birnin Bauchi.
Sai dai kotun ta ba wa waɗanda aka yanke wa hukuncin damar biyan tarar naira dubu 370 kowannensu a madadin ɗaurin gidan yarin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Ya ce kamen ya biyo bayan ƙorafin da kwamitin zaman lafiya da tsaro na unguwar Dim ya shigar a ranar 14 ga watan Oktoba, kan sake ɓarkewar ayyukan daba a yankin.
A cewarsa, jami’an ’yan sanda tare da jami’an tsaron al’umma sun kai samame wani wurin ɓuya da ake zargin masu laifin ke amfani da shi da sanyin safiyar ranar 15 ga watan Oktoba, inda suka kama mutane tara.
Ya ƙara da cewa jami’an sun ƙwato makamai da suka haɗa da adduna, wuƙaƙe da sanduna, baya ga wasu haramtattun abubuwa da aka samu a wurin.
Kakakin ya ce bayan kammala bincike, an gurfanar da takwas daga cikin waɗanda aka kama a gaban kotu, inda kotun ta same su da laifi bayan sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi maraba da hukuncin, tare da kira ga mazauna jihar da su riƙa kai rahoton sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen dakile aikata laifuka.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin yaƙi da daba da sauran laifuka, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

