Shugaban matasan jam’iyyar NDC Kwankwasiyya na mazabar Dandago da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano, Hon. Aminu La Boys, ya bayyana cewa da ba don Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba, da mutane da dama ba su san Muhammad Sabo Bakin Zuwo a fagen siyasar Kano ba.
Aminu La Boys ya ce Sabo Bakin Zuwo ya samu karɓuwa a siyasar jihar ne bayan haɗuwarsa da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya kuma bayyana cewa, duk da rikicin da ke faruwa a cikin jam’iyyar NDC, Sabo Bakin Zuwo ya nuna adalci ta hanyar barin wasu muƙamai a hannun waɗanda ke riƙe da su, domin samar da haɗin kai da samun nasarar jam’iyyar.
La Boys ya ƙara da cewa, wasu daga cikin masu takara da aka sauya sunayensu ne ke rura wutar rikicin da ake fuskanta a jam’iyyar, yana mai cewa irin waɗannan matakai na iya kawo cikas ga haɗin kan mambobinta.
Aminu La Boys ya kuma bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar Gwale, Hon. Aminu Warkal, inda ya ce babu wanda ya fi dacewa da jagorantar al’ummar Gwale a majalisar kamar shi, duba da jajircewarsa da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen taimaka wa matasa.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jam’iyyar NDC Kwankwasiyya haɗin kai da goyon baya domin cimma manufofinta da samun nasara a harkokin siyasa.

