Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanar da cewa gwamnatinsa ta yi rangwamen haraji da kuɗaɗen fito da suka kai naira tiriliyan 3 kan man fetur, a wani mataki na rage tsadar mai da kuma sauƙaƙa wa ’yan Najeriya matsin tattalin arziki.
Tinubu ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen sufuri da kuma rage nauyin tsadar rayuwa da ke addabar jama’a.
Haka kuma, an bayyana cewa kamfanin NNPC Retail zai dakatar da karɓar ribar da yake samu daga sayar da man fetur na tsawon kwanaki 30, domin sayar da shi a kan farashin da ya saya, a wani yunƙuri na rage tasirin hauhawar farashin man fetur a kasuwa.
Gwamnatin ta kuma bayyana aniyarta ta faɗaɗa amfani da iskar gas na CNG a harkokin sufuri, domin samar da madadin man fetur da zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da sauƙaƙa wa jama’a rayuwa.

