Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta kai ziyara ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da tattauna hanyoyin magance matsalar shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Shari’a ta Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta gana da kwamandan NDLEA na jihar Kano, Dahiru Yahaya Lawal, da sauran jami’an hukumar a ranar Juma’a.
Da yake jawabi yayin ziyarar, kwamishina na biyu a hukumar Shari’a , Sheikh Ali Danabba, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin biyu domin zurfafa ƙoƙarin yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
Sheikh Danabba ya kuma yaba wa kwamandan NDLEA bisa ƙoƙarin da yake yi wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da sauran abubuwan da ke jawo maye a Kano.
A nasa jawabin, kwamandan NDLEA na Kano, Dahiru Yahaya Lawal, ya gode wa hukumar Hisbah bisa ziyarar, tare da kira ga malaman addinin Musulunci da su ƙara wayar da kan al’umma game da illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Ya buƙaci limaman masallatai da su yi amfani da hudubar Juma’a wajen faɗakar da al’umma kan illolin shaye-shaye da muhimmancin nisantar miyagun ƙwayoyi.
A yayin ziyarar, Sheikh Ali Danabba ne ya jagoranci sallar Juma’a a harabar hedikwatar NDLEA ta jihar Kano.
Daga bisani, jami’an NDLEA sun zagaya da tawagar hukumar Hisbah zuwa wuraren tsare waɗanda ake zargi da aikata laifuffukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, inda mambobin tawagar suka ba waɗanda ake tsare da su shawarwari tare da yi musu nasiha.

