Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da gabatar da karin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai jimillar Naira tiriliyan 1 da biliyan 201, tare da umartar a tura kudirin zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin nazari da ɗaukar matakin da ya dace.
An amince da matakin ne yayin taron Majalisar karo na 41 da aka gudanar ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, a Malam Aminu Kano House da ke Asokoro, Abuja, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr. Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Kano.
Dr. Waiya ya ce kwaskwarimar kasafin kuɗin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin samar da ƙarin kuɗaɗen gudanar da ayyukan raya jihar da kuma bunƙasa muhimman fannoni da suka shafi rayuwar al’ummar Kano.
A wani ɓangare na matakan da Majalisar ta amince da su, an ware jimillar Naira biliyan 144 da miliyan 5 domin aiwatar da ayyukan raya jihar a fannoni daban-daban.
Ma’aikatar Ayyuka ce ta samu kaso mafi yawa, inda aka ware mata sama da Naira biliyan 84 da miliyan 975 domin aiwatar da ayyukan hanyoyi da gine-ginen gwamnati.

