Tsohon Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare na Jihar Kano, kuma tsohon Shugaban Kwamitin Tsarawa da Raba Filayen Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Dan Azumi Gwarzo, ya ce bai kamata malamai su rika kafirta ko la’antar Musulman da ke yin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) ba, domin hakan na iya ƙara raba kan al’ummar Musulmi.
Dan Azumi Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, inda ya yi magana kan yadda ake kallon bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW) a tsakanin al’ummar Musulmi.
Ya ce akwai wasu malamai da ke la’antar masu gudanar da bukukuwan Maulidi ko nuna farin ciki da watan da aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), lamarin da ya ce yana ƙara ta’azzara rarrabuwar kai tsakanin Musulmi.
A cewarsa, bai dace malamai su rika hawa mimbari suna furta kalaman da za su kai ga kafirta ko zargin kafirci ga Musulman da suke bin wata darika ko kuma masu gudanar da Maulidi ba.
Ibrahim Dan Azumi Gwarzo ya ƙara jaddada muhimmancin watan da ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW), yana mai cewa babu wani wata ko rana da ta kai ranar haihuwar Annabi (SAW) daraja.
Ya ce hakan ne ya sa wasu Musulmi ke nuna farin cikinsu da zagayowar wannan lokaci, tare da shirya tarukan Maulidi, musamman a makarantun Islamiyya.
A ƙarshe, Dan Azumi Gwarzo ya yi kira ga masu shirya tarukan Maulidi da su riƙa ƙoƙarin tsaftace tarukansu daga abubuwan da ba su dace ba, musamman gaurayawar maza da mata, tare da kauce wa duk wani abu da bai dace da tarbiyyar Musulunci ba.

