Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a yau, Lahadi, domin fara hutun shekara na tsawon makonni uku a ƙasashen Turai.
A cewar sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar,birnin London da ke ƙasar Birtaniya ne zai kasance waje na farko ta Shugaba Tinubu zai yada zango domin fara hutun.
Sanarwar ta bayyana cewa hutun wani ɓangare ne na hutun shekara-shekara da shugaban ƙasar ke samu.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala hutun, inda zai ci gaba da ayyukan gwamnati tare da shiga shirye-shiryen kamfen ɗin zaɓen da aka tsara gudanarwa a watan Janairun 2027.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya sanya hannu kan sanarwar a ranar 30 ga Agusta, 2026.

