Daga Kabiru Muhammad Getso.
Shugaban riko na kwalejin Fasaha ta Husaini Adamu Federal Polytechnic Kazaure, Injiniya Dakta Bashir Ahmad Danzomo, ya bayyana alfaharinsa da daliban kwalejin bisa yadda suke samun nasara a karatunsu da kuma ci gaba da karatu a manyan jami’o’i da sauran manyan makarantu a sassan Najeriya.
Engr. Dr. Bashir Ahmad Danzomo ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga jajircewar kwalejin wajen tabbatar da ingantaccen tsarin koyo da koyarwa, tare da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa dalibai damar samun ilimi mai inganci.
Ya bayyana cewa kwalejin tana da sassa shida na ilimi, wadanda kowannensu ke da kwasa-kwasai daban-daban da ake koyarwa bisa tsarin da hukumomin da suka dace suka amince da shi.
Shugaban kwalejin ya shaida hakan ne a ofishinsa a lokacin zantawa da manema labarai inda ya ce baya ga shirye-shiryen karatu, makarantar tana da kwararrun malamai da suka samu horo na musamman, wadanda ke amfani da kwarewarsu wajen bai wa dalibai ilimin da ya dace da bukatun zamani.
Ya kuma yi kira ga daliban da suka samu gurbin karatu a kwalejin da su dauki karatunsu da muhimmanci, su kasance masu jajircewa da bin doka da oda, domin ilimin da suke samu a yau shi ne ginshikin makomarsu da ta al’umma baki daya.
Da yake magana kan nasarorin da aka samu tun bayan da ya karbi ragamar shugabancin riko na kwalejin, Engr. Dr. Bashir ya ce ya samu cikakken hadin kan malamai da sauran ma’aikata wajen gano manyan matsalolin da ke fuskantar makarantar da kuma daukar matakan magance su.
Ya ce daga cikin abubuwan da aka fara mayar da hankali a kansu akwai kara yawan ma’aikata, musamman jami’an tsaro, domin tabbatar da tsaron dalibai da kadarorin kwalejin.
Ya kara da cewa an gudanar da gyare-gyare a wurare daban-daban na makarantar, ciki har da samar da isasshen ruwan sha ga daliban da ke zaune a gidajen kwanan dalibai.
A cewarsa, an kuma kara mayar da hankali wajen tsaftace harabar kwalejin da inganta muhallin makarantar, domin samar da yanayin da zai karfafa sha’awar dalibai da malamai wajen gudanar da harkokin koyo da koyarwa.
A wani bangare, Shugaban kwalejin ya yabawa Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma, Sanata Babangida Husaini Walin Kazaure, bisa irin gudunmawar da yake bai wa makarantar.
Ya ce Sanatan ya taimaka wajen samar da wani katafaren bangare na kwalejin tare da samar da kayayyakin da ake bukata, wanda ya ce hakan zai kara bunkasa harkokin ilimi a makarantar.
Haka kuma, Engr. Dr. Bashir Ahmad Danzomo ya yabawa shugabannin kananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi, bisa daukar nauyin wasu dalibai daga yankunansu domin ba su damar samun ilimi a kwalejin.
Ya ce irin wannan tallafi ba wai kawai yana taimakawa daliban da suka amfana bane, har ma yana bayar da gudunmawa wajen bunkasa ilimi da samar da kwararrun matasa da za su amfani al’umma a nan gaba.
Shugaban kwalejin ya yi kira ga sauran al’umma, musamman masu hannu da shuni, da kungiyoyi da ‘yan kasuwa, da su ci gaba da tallafa wa harkar ilimi da matasa.
Ya ce zuba jari a ilimi na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa, tare da samar da makoma mai kyau da kuma rage wasu matsalolin da ke addabar al’umma.
A karshe, Engr. Dr. Bashir Ahmad Danzomo ya jaddada cewa hadin kan gwamnati, makarantu, iyaye da sauran al’umma shi ne ginshikin samun ingantaccen ilimi da samar da matasa masu ilimi, kwarewa da kishin kasa.

