Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima,ya ce Najeriya na fara nuna alamun dawowa kan turbar cigaba da wadatar arziki ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen da gwamnatin ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau a ƙasar nan.
Shettima ya yi wannan furuci ne yayin da ya miƙa takardar sake neman takarar shugaban ƙasa Tinubu domin shiga zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa, duk da irin ƙalubalen da ‘yan Najeriya suke fuskanta a sakamakon wasu matakan tattalin arziƙi da gwamnati ta ɗauka, yanzu abubuwa sun fara sauyawa, inda ya ce ana fara ganin sauƙin matsin tattalin arziƙi tare da bunƙasar wasu fannoni na rayuwa da harkokin kasuwanci.
Ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta duƙufa wajen gina ƙasa mai ɗorewa ta hanyar inganta tattalin arziƙi, ƙarfafa tsaro, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa rayuwar al’umma.
Shettima ya kuma nuna cikakken kwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta sake samun goyon bayan ‘yan Najeriya a zaɓen 2027, yana mai cewa gwamnatin mai ci ta na aiki tukuru domin ganin ƙasar ta samu ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya.

