Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya shaida cewa suna cikin damuwa yadda ake jula jula da jagoran Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso cikin Jamiyyu daban daban a cikin kasa da wata daya.
Kwamared Waiya ya shaida hakan ne a wata hira ta musamman da ya jagoranta da kafafen yada labarai a daren Lahadi.
TST Hausa ta rawaito cewa ,kwamishinan yace akwai damuwa yadda Kwankwaso yake ta tsalle tsalle a cikin Jamiyyu maimakon ya samu lokaci ya huta.
Kwamishinan yace yanzu gaskiya tayi halinta kan makomar siyasar gwamnan Kano Alhaji Abba Kabiru Yusuf.
Yace da zuciya gwamnan ya koma APC kuma masu sukarsa yanzu sun fahimci hakan

