Tsohon ministan tsaro,kuma tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso , ya taya gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, tare da yaba masa bisa gudummawar da ya bayar tsawon shekaru a hidimar Jihar Kano.
A cikin sakon taya murnar da ya fitar,Kwankwaso ya tuno da dogon tafiyarsu ta siyasa tare, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi aiki a muhimman mukamai daban-daban a ƙarƙashin jagorancinsa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tura-ta-kai-bango-tsakanin-mu-da-yan-bindiga-da-ke-shigowa-kano-gwamna-yusuf/
Ya bayyana cewa Gwamnan ya fara ne a matsayin Mataimakinsa na Musamman a zangonsa na farko a matsayin gwamna da Minista, daga bisani ya zama babban Mataimakin Kansa, sannan daga baya ya rike mukamin Kwamishina a zangonsa na biyu.
Kwankwaso ya ce a duk waɗannan mukamai, Abba Kabir Yusuf ya nuna jajircewa, da biyayya da ƙwazo wajen aiwatar da hangen nesa da shirye-shiryen ci gaba da suka shafi bunƙasar Jihar Kano musamman bayan zama gwamna.
Ya ƙara da cewa Allah Ya ƙaddara masa kai wa matakin Gwamnan Jihar Kano ne sakamakon gogewa da kwarewar da ya tara tsawon shekaru a harkar mulki da siyasa.
Tsohon Ministan ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba Gwamna Abba Kabir Yusuf tsawon rai cikin koshin lafiya, hikima da basira a wannan sabuwar shekarar rayuwarsa, domin ci gaba da jagorantar al’ummar Kano zuwa cigaba mai ɗorewa.

