ƙaramin yaron da yayi tashe a shafukan sada zumunta na Zamani dake kuka kuma ya fashe da dariya lokaci guda mai suna Albert Ofosu Nketia, ɗan ƙasar Ghana, ya cika shekara 12 da haihuwa a duniya.
Karamin yaron ya shiga zukatan al’ummar duniya bayan wani gajeren bidiyo da ya bazu sosai a shafukan sada zumunta, inda aka ganshi yana kuka sannan nan take ya fashe da dariya.
Bidiyon, wanda aka fara yadawa a farkon shekarar 2023, ya sanya mutane da dama dariya tare da mamaki, sakamakon yadda yaron ya sauya yanayi cikin kankanin lokaci.
Wannan lamari ne da ya sa aka fara kiransa da suna “Funniest Albert” a yanar gizo.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/duk-da-na-cika-shekara-100-a-duniya-da-zaa-hada-min-dukiyar-najeriya-ina-so-tanko-yakasai/
Rahotanni sun nuna cewa Albert ya fito ne daga yankin Ashanti na kasar Ghana, kuma iyalinsa na zaune ne a birnin Kumasi.
A cewar mahaifiyarsa, lamarin ya faru ne a lokacin da Albert ya fara kuka saboda bai samu abincin da yake so ba, sai dai daga bisani kakarsa ta raira masa waka domin kwantar masa da hankali, wanda hakan ya sa ya juya daga kuka zuwa dariya.
A lokacin da bidiyon ya yi fice, Albert yana da kimanin tsakanin shekaru 9 zuwa 10 kuma daga wannan lokaci ya zama ɗaya daga cikin fitattun yara da aka fi amfani da hotunansu a meme da bidiyoyin barkwanci a kafafen sada zumunta kamar TikTok, Facebook da Instagram.
Yanzu haka, duk da cewa ana ci gaba da ambaton sa a shafukan yanar gizo, iyalinsa sun bayyana cewa suna kula da rayuwarsa kamar kowane yaro, tare da tabbatar da cewa shahararsa ba ta hana shi samun tarbiyya da ilimi ba.
A yayinda yake bikin cikarsa shekarar 12 iyalansa na fatan rayuwarsa ta sake haskawa a duniya.
Lamarin Funniest Albert ya sake nuna yadda kafafen sada zumunta ke iya ɗaga kowa ko da yaro ya zama sananne a duniya cikin kankanin lokaci, tare da yada farin ciki ga miliyoyin mutane.

