Babban Limamin masallacin Juma’a na Usman Bn Affan dake Unguwar Gadon Kaya cikin karamar hukumar Gwale Dr. Aliyu Yunus, ya jaddada cewa masu tsayuwar sallar dare (Qiyamul-Layl) da kuma wadanda ke kiyaye sallar Asuba cikin jam’i su na daga cikin mutanen da Allah ya yi wa alkairi a duniya da lahira.
Dr.Aliyu Yunus ya shaida hakan ne a yayinda yake gabatar da hudubarsa ta Sallar Juma’a.
Dr. Yunus ya bayyana cewa tsare wadannan ibadoji ba wai kawai suna gina zuciya ba ne, har ma suna ba wa mumini natsuwa,da kusanci ga Ubangiji.
Ya ce masu tsayuwar dare na samun rahamar Allah mai yawa, domin wannan sallah tana kawar da zunubi, tana tsarkake zuciya, kuma tana bude kofofin arziki da kariya.
Malamin ya kara da cewa sallar Asuba kuwa ita ce ginshiƙin farkon rana ga musulmi, wacce ke sa albarka cikin ayyukan yau da kullum.
Ya ce halin da wasu ke ciki na sakaci da wannan sallah na kara nisantar da su daga albarkar da Allah Ya tanadar ga masu tsare ta.
Malamin ya kuma bayyana cewa Allah Ya yi wa masu tsare lokutan salloli alkawarin nasara kamar yadda ya zo a Suratul Mu’minun.
“Lalle ne sun yi nasara muminai… wadanda suke tsare sallarsu.”
Dr. Yunus ya yi kira ga musulmi su rika kokarin tashi cikin dare domin yin ibada, ko da ba duka daren ba.
Haka kuma ya shawarce su da kada su bari sallar Asuba ta wuce su, domin ita ce gwaji mafi sauƙi da ke nuna yadda imani ke aiki a zuciyar bawa da kuma kunyata shaiɗan a kowacce rana da kunce kulle kullensa akan bayin Allah.
Ya kammala da cewa duk wanda ya daure ya kiyaye wadannan sallah-sallah biyu zai more kyakkyawar rayuwa a duniya, tare da samun lada marar iyaka a lahira.
Daga nan yace kwanciya akan lokaci da kiyaye amfani da abinda zai hana mutum bacci da wuri musamman rage amfani da wayar Salula na daga cikin abubuwan zasu janyo mutum zai rika tashi Sallar Asuba.

