Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga matasa da su rungumi sabon shirin kirkire-kirkiren zamani da aka kaddamar domin inganta fasaha da samar da damar ci gaban tattalin arziki a jihar.
Gwamna Yusuf yace gwannati tayi nisa wajen horas da matasa hanyoyin dogaro da kansu tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.
Gwamna Yusuf wanda ya samu wakilcin kwamishinan Yaɗa Labarai da al’amuran cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya shaida hakan ne a yayin taron kaddamar da shirin kirkire kirkire na shekara shekara mai taken “Buɗe Ƙarfinsa Najeriya a Fannin Kirkire-Kirkire: Cibiyoyi a Matsayin Injinan Sauyi da Hanyoyin Tallafa wa Masu Kirkira.”
A cewar Kwamishinan, shirin na da nufin karfafa cibiyoyin kirkire-kirkire, da koyar da matasa kwarewar fasahar zamani tare da samar musu da hanyoyin haɗin guiwa da shirin tallafin gogaggun kwararru domin inganta basirar su.
Ya bayyana cewa shirin yana samun goyon baya daga Hadakar Jamus da Tarayyar Turai (EU) tare da haɗin guiwa da sauran masu ruwa da tsaki a fadin ƙasar nan.
Ya ce wannan tallafi zai taka rawa wajen bunkasa sabbin fasahohi da samar da mafita ga matsalolin da ke addabar al’umma.
Kwamared Waiya ya ce gwamnatin Kano tana da yakinin cewa matasan jihar na da hazakar da za ta iya kai jihar ga zama jagora a harkar kirkire-kirkire a Najeriya, musamman idan suka amfana da dabarun da wannan shiri zai koyar.
Shirin, wanda ya kunshi horo da kayan aiki na zamani, yana nufin inganta ci gaban fasaha, samar da sababbin hanyoyin samun ayyukan yi, da taimakawa wajen faɗaɗa tattalin arziki ta hanyar ƙirƙirar sabbin masana’antu da ra’ayoyi masu amfani.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da kudirinta na ci gaba da marawa matasa baya, tare da samar musu da ingantattun hanyoyi da za su taimaka wajen gina makoma mai dorewa a fannoni daban-daban.

