Gwamnatin Jihar Kwara ta rufe makarantun gwamnati a kananan hukumomi huɗu,na jihar sakamakon tsananin hare-haren ’yan bindiga da suka ƙara kamari a jihar.
A cikin sanarwar da Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta jihar ta fitar, an bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare rayukan ɗalibai da malamai, tare da maye gurbin malamai zuwa wuraren da ake ganin sun fi aminci.
Gwamnatin ta ce matakin na wucin gadi ne har sai an samu ƙaruwar tsaro.
A wasu yankuna kamar Babanla, da Baba Sango,da Sangbe da Oke-Ode, mazauna sun yi ta korafi kan yadda ’yan bindiga ke amfani da dazuzzukan yankin a matsayin mafaka.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar ta sake jaddada bukatar kafa sansanin soji na dindindin a yankin, domin fatattakar ’yan bindiga da suka mamaye dazukan Baba Sango.
’Yan majalisar dattawa daga yankin sun goyi bayan wannan kira, tare da neman gwamnatin tarayya ta gaggauta kafa sansanin.
Rahotanni sun nuna cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa rundunar sojin Najeriya umarnin kau da sansanonin ’yan ta’adda a dazuzzukan jihar, tare da tura karin dakaru da kayan aiki don aikin fatattaka.
Gwamnatin jihar ta kuma sanar da soke harajin Kungiyar iyaye da malamai ta PTA a dukkan makarantun gwamnati, da kuma fitar da tallafin shekara-shekara domin ci gaba da gudanar da ayyukan ilimi duk da matsalar tsaro.

