A yayin da zaben 2027 ke kara matsowa, wasu daga cikin manyan jiga-jigan siyasa a Jihar Kano musamman matasa na matsa lamba kan bukatar fitaccen dan siyasa a jihar Arc.Aminu Dabo, da ya fito takarar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC.
Masu kiran da suka ce lokacin bayyana kansu baiyi ba sun cewa Kano tana bukatar ingantaccen jagora mai hangen nesa, tare da kwazon aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta tsaro,da habaka tattalin arziki da kuma kawo cigaba mai dorewa.
A cewar su, tarihin aikin Aminu Dabo da gogewarsa a fannoni daban-daban ya nuna cewa yana da jajircewar da ake bukata wajen jagorantar jihar a wannan zamani.
Aminu Dabo wanda ya taba rike hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta kasa, tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya nada shi a watan Afirilun shekarar 2002 zuwa watan Oktoba na Oktoban 2003
Arc.Dabo a Yanzu haka ya kafa manyan makarantu guda uku na kiwon lafiya tun a shekarar 2013 wadanda suka bada gudun mowa wajen ciyar da Kano gaba a fannin kiwon lafiya.
Duk da cewa har yanzu Aminu Dabo bai bayyana matsayinsa kan ko zai tsaya takara ba,amma magoya bayansa sun ce za su ci gaba da karfafa masa guiwa har sai ya amsa kiran jama’a ya nemi kujerar Gwamna a Kano a shekarar 2027.

